Jirgin ruwa ya kife da mutane 100 a Taraba

Image caption An sha samun tashin hankali na kabilanci tsakanin kabilun biyu

Hukumomi a jihar Taraba da ke Najeriya sun ce sojin ruwa na kasar na ci gaba da aikin ceto, bayan wani jirgin ruwa ya kife da mutane fiye da 100.

Akasarin wandada lamarin ya rutsa da su mata ne da kananan yara, a lokacin da suke kokarin tsere wa daga wani harin da wasu 'yan bingiga suka kai kauyen Dampar a ranar Talata.

Rahotanni sun ce akalla mutane fiye da 10 suka mutu, wasu da dama suka jikkata a harin da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen na Dampar da ke karamar hukumar Ibi.

Mazauna yankin dai na zargin 'yan kabilar Taroh da kai harin a kauyen na Dampar, amma 'yan kabilar na Taroh sun sha musanta zargin.