An kori hafsoshin Soja hudu a Iraqi

Hakkin mallakar hoto AFP

Firaministan Iraqi, Nouri al-Maliki ya kori manyan hafsoshin sojan kasar hudu sakamakon faduwar birnin Iraqi na biyu, Mosul zuwa hannun 'yan Sunni masu tada-kayar-baya a makon jiya.

Mutane a Bagadaza babban birnin Iraqi na tara abinci da ruwan sha yayin da ake ganin 'yan tada-kayar-bayan na dada kusantar birni.

Tun da farko dakarun tsaron Iraqi da sojan sa-kai 'yan shi'ah sun dakile yunkurin mayakan da kungiyar ISIS ke jagoranta a birnin Baquba, mai nisan kilomita sittin daga Bagadaza.

Wani dan siyasa a birnin, Sa'ad Metalby ya ce sun amince a shigar da wani gagarumin kaso na mayaka 'yan sa-kai cikin dakarun soja da ke yankunan da suka kewaye birnin Bagadaza don tabbatar da cewa ba wani bako.