Obama na iya kauce wa Majalisa kan Iraqi

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban jam'iyyar Republican a majalisar dattijan Amurka ya ce Shugaba Obama ya yi imani cewa ba ya bukatar amincewar majalisun dokokin kasar a kan duk wani matakin soji da ya yanke shawarar dauka game da rikicin Iraqi.

Mr. Mitch Mac-Connel ya bayyana haka ne bayan wani taro da shugabannin majalisar dattijan hudu suka gudanar da Barak Obama kan batun daukar matakin soja a rikicin Iraq.

Gwamnatin Iraqi ta nemi tallafin Amurka wajen kai hare-hare ta sama don fatattakar 'yan Sunni masu gwagwarmaya da suka kwace birane da dama a yankin arewacin kasar.

Wani wakilin BBC ya ce Mr.Obama na da zabi daban-daban kama daga kai farmaki ta sama ya zuwa ba da karin horo, sai dai abin da Amurka ke iya yi kadai shi ne aikewa da jiragen yaki marasa matuka zuwa kasar.