Sarkin Kano ya nada sabon Waziri

Image caption Sabon Wazirin Kano, Malam Saad Shehu Gidado

Sabon Sarkin Kano Mai martaba Alhaji Muhammad Sanusi II ya nada sabon Wazirin Kano, Malam Sa'ad Shehu Gidado.

Wannan ne dai babban nadi na farko da Sarkin ya yi tun bayan da ya hau karagar mulki a farkon watan Yuni.

Karo na biyu kenan da aka nada Wazirin Kano a cikin makonni uku, wanda da farko lamarin ya janyo takaddama tsakanin gwamnatin Kano da masarautar ta Kano, zamanin Marigayi Sarki Ado Bayero.

Sai dai daga bisani Wazirin da aka nada Sheikh Nasiru Mohammed Nasir ya yi murabus.

Karin bayani