Nijar ta bullo da shirin samar da ayyuka

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce ta bullo da wani shirin samar da ayyukan yi ga matasa fiye da dubu 6 da 500 a fadin kasar.

Za a fara shirin na shekaru biyu, bana a matsayin gwaji inda zai ci biliyan 7 na CFA a wani bangare na alkawarin da shugaban kasar Alhaji Mahamadu Isufu ya yi na samar da guraben aiki dubu 50 kowacce shekara.

Da yake karin haske kan shiri, Ministan samar da aikin yi, Mallam Salisu Ada ya ce shirin zai shafi matasa masu karanci da marasa ilmin Boko a fadin kananan Hukumomin 265 da ke fama da rashin aikin yi.

Ya ce a karkashin shirin kowanne matashi zai rika karbar jaka hamsin duk wata tare da sauran tallafin aikin yi daga gwamnati.

Tuni dai matasan kasar suka yi maraba da wannan shiri inda suka yi fatan tabbatarsa ba tare da shigar da siyasa ko kasancewa wani romon baka daga 'yan siyasa ba