Ba maganar juyin mulki a Nigeria - Soji

Babban Hafsan sojin Najeriya, ya yi watsi da rade-radin cewa mai yiwu wa sojoji su yi juyin mulki, saboda yawan tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta.

A cikin wata sanarwa da hukumar wayar da kan al'umma ta kasar NOA ta fitar, Air Chief Marshall Alex Badeh ya ce batun juyin mulki a Nijeriya bai ma taso ba, saboda sojojin Nijeriya suna kare tsarin dimukradiyya.

Alex Badeh ya ce sojojin kasar jigo ne a kafuwar tsarin dimukradiyya, don haka za su ci gaba da kare ta, ya kara da cewa aikin soji ne kare dimokradiyya amma ba kawo mata cikas ba.

Rundunar sojan kasar na shan suka kan gazawarta na magance hare-haren kungiyar Boko Haram, da gano 'yan matan Sakandaren Chibok fiye da 200 da kungiyar ta sace sama da watanni biyu.

Wasu mutane na ganin cewa furucin Babban hafsan sojan a wannan lokaci ka iya cusa fargaba maimakon rage ta musammam ganin yadda kasar ke tunkarar babban zabe a shekara mai zuwa.