Yaki ya daidaita mutane miliyan 50 a duniya

Wasu 'yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption 'yan gudun hijira dubu 40 ne ke zaune a Nijar bayan da suka tsere wa rikicin Boko Haram a Nigeria

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da yaki ya daidaita ko kuma aka muzguna musu a sassa daban-daban na duniya ya zarce miliyan 50 a bara kadai.

Wannan shi ne alkaluma mafi girma da aka taba samu tun bayan yakin duniya na biyu, sai dai hukumar ta ce kusan mutane miliyan 17 sun tsere ne daga kasashensu, yayin da fiye da mutane miliyan 33 na zaune ne cikin kasashensu bayan da yaki ya sa sun tsere daga gidajensu.

Akasarin mutanen sun shafe shekaru da dama a sansanonin 'yan gudun hijira, inda hukumar ta ce karuwar adadin mutanen da ke gudun hijira wata babbar alama ce ta gazawa wajen hana afkuwar tashe-tashen hankula.

Asarar da yaki da kuma azabtarwa ke haifar wa ga al'umma

51.2m

mutanen da aka tilastawa barin gidanjensu a fadin duniya

  • 2.6m mutanen da suka tsere daga Afghanistan

  • 1.6m yan gudun hijiran Pakistan

  • 1.2m mutane masu neman mafakar siyasa a fadin duniya

GETTY

Rahotanni sun ce yanzu haka akwai 'yan gudun hijira kimanin 40,000 da ke zaune a jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, bayan sun tsere wa rikicin Boko Haram daga Nigeria.

Kungiyoyin agaji da suka hada da Hukumar samar da abinci ta duniya da kungiyar ba da agaji ta Geneva na kokarin tallafa wa 'yan gudun hijirar da kayan abinci da kuma sauran kayan masarufi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service