An kashe mutane 21 a harin bam a Yobe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta hallaka dubban mutane a Nigeria

A Nigeria wata majiya a asibitin Damaturu ta shaida wa BBC cewa mutane 21 ne suka mutu a harin bam din da aka kai wajen kallon kwallo.

A cewar majiyar kuma wasu mutane 27 ne suka jikkata a harin na ranar Talata a jihar Yobe.

Ko da yake wasu majiyoyin dakarun kasar sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 ne, yayin da wasu kusan 30 suka samu raunuka sakamakon harin bam a wani gidan kallo.

Babu wata kungiya da ta amsa laifin kai wannan harin a Damaturu babban birnin jihar, amma kuma al'ummar jihar Yobe na zargin kungiyar Boko Haram da kai wannan harin.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Yobe Markus Danladi ya ce kawo yanzu komai ya lafa, sannan ya kara da dama can an haramta bude gidajen kallo a jihar kuma inda aka kai harin, masu gidan kallo sun sabawa doka ne.

Gidajen kallo na da farin jini a Nigeria musamman a wannan lokacin na gasar cin kofin duniya.

Wasu jihohin Nigeria kamar su Adamawa da Filato sun haramta bude gidajen kallo a lokacin gasar cin kofin duniya saboda zargin cewar 'yan Boko Haram za su iya kai hari kan jama'a a wuraren.

'Yan Boko Haram sun addabi yankin arewacin Nigeria musamman jihohin da ke arewa-maso-gabas inda nan ne cibiyar kungiyar ta ke.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidajen kallo na da farin jini a Nigeria

Karin bayani