An rufe asusun gwamnatin jihar Adamawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamna Nyako na fuskantar yunkurin tsigewai daga majalisar dokokin jihar

Gwamnatin Adamawa a Nigeria ta ce Hukumar EFCC ta rufe asusun ajiyarta na bankin Zenith.

Attorney Janar na Jihar, Ibrahim Tahir ya ce ya samu kwafin sanarwa daga Babban Ofishin Bankin na rufe asusun wanda Hukumar EFCC ta aike masa.

Wannan batun na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan majalisar dokokin Jihar ke yunkurin tsige gwamnan Jihar Admiral Murtala Nyako.

Daraktan yada labarai na Jihar Adamawa Ahmed Sajoh ya ce gwamnatinsu ta yi mamaki game da rufe asusun ajiyar jihar lamarin da ka iya shafar rayuwar al'ummarta wadanda tattalin arzikinsu ya dogara a kan albashi daga gwamnati.

Ya ce suna nazari kan lamarin don daukar matakin da ya dace.

Sai dai, BBC ta yi kokarin jin ta-bakin Hukumar EFCC don jin bahasinta game da wannan batu ba tare da nasara ba.