Charles Taylor ya kalubalanci daurinsa a Burtaniya

M. Charles Taylor Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr. Taylor na zaman wakafi a kurkukun Frankland, bayan wata kotu ta musamman kan Saliyo ta yanke masa hukuncin shekaru 50

Tsohon shugaban Liberia, Charles Taylor, ya shigar da kara kotu yana kalubalantar zaman kurkukun da ya ke yi a Birtaniya.

Lauyan mista Taylor ya ce an take masa hakkinsa, saboda gidan kason da yake zaune a Ingila ya yi nisa sosai da Afirka, ta yadda matarsa da 'ya'yansa 15 ba za su iya zuwa ba.

A cewar lauyan, kamata yayi Charles Taylor ya yi zaman kurkukun a Rwanda, tare da sauran wadanda aka same su da laifi tare.

Tsohon shugaban na zaman daurin shekaru hamsin ne, bayan kotu ta same shi da hannu a aikata laifin yin fyade, da kisan kai da kuma daukar kananan yara aikin soja a lokacin yakin Saliyo.