An hana gwamnonin APC shiga Ekiti

Image caption APC ta lashi takobin kwace mulki a wajen PDP a 2015

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria ta ce jami'an tsaro sun hana gwamnoninta uku zuwa garin Ado-Ekiti domin halartar gangamin yakin neman zabe na karshe na zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar ranar Asabar.

Wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na Jam'iyyar, Alhaji Lai Muhammad ta ce, gwamnonin da aka hana zuwa wajen taron sun hadar da Rotimi Amaechi na jihar Rivers, da Adams Oshiomole na Edo.

Sanarwar jam'iyyar ta APC ta kuma ce, yayin da aka hana jerin gwanon motocin gwamnan Rivers wucewa, an kyale na ministan tsaro da na minista mai kula da al'amuran 'yan sanda sun wuce.

Kawo yanzu ba mu samu martani daga jami'an tsaro game da lamarin ba.

Jam'iyyun adawa a Nigeria sun sha zargin cewar gwamnatin tarayya ta PDP na muzguna musu.

Karin bayani