Zaben shugaban kasa a Mauritania

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin gwamnati da yunkurin maida Mauritania ta farar fata zalla

'Yan kasar Mauritania sama da miliyan daya da dubu dari hudu ne za su nufi rumfunan zabe ranar Asabar don kada kuri'unsu a zaben sabon shugaba.

Shugaban kasar mai ci, Mohammed Ould Abdel Aziz wanda ake ganin shi ne zai lashe wannan zabe na fuskantar kalubale daga 'yan takara 4, da suka hadar da wata Mace da kuma wani mai fafutukar yin watsi da dabi'ar bauta.

Manyan jam'iyun adawa a kasar sun ce za su kaurace wa zaben, inda suka bukaci a dakatar da shi ya zuwa lokacin da za a samu daidaito, saboda zargin tafka murdiya tun kafin kada kuri'u daga shugaba Ould Abdel Aziz.

Babban batun da ya mamaye wannan zabe shi ne zargin ci gaba da al'adar bauta, inda kungiyoyin kare 'yancin dan'adam ke sukar lamirin gwamnatin shugaba Ould Abdel Aziz a kan rashin tabuka abin kirki wajen kakkabe bauta