Batanci: Uganda ta dakatar da talabijin

Image caption Museveni mai shekara 69, da yake mulki tun 1986, na daga shugabannin Afrika da suka dade a kan mulki.

Gwamnatin Uganda ta dakatar da wani gidan talabijin halarta da watsa abubuwan da shugaban kasar ke gudanarwa bayan tashar ta nuna shi ta ce yana barci.

Kakakin gwamnatin, Ofwono Opondo ya tabbatar da daukar matakin a kan gidan talabijin din mai zaman kansa na NTV Uganda.

Gwamnatin ta musanta cewa shugaban yana barci ne a lokacin da aka dauke shi yayin zaman majalisar dokokin kasar.

Jam'in kula da cibiyar yada labarai ta gwamnatin, Dennis Katungi, ya ce, ''sun san shugaban yana da wannan dabi'a ta rufe ido yana tunani, amma suka ce barci yake.''

Mr Katungi ya ce, ''dakatarwar ba ta dun-dun-dun ba ce, an yi hakan ne domin horonso.''

Sai dai gidan talabijin din na NTV ya ce ba a sanar da shi ba a kan dakatarwar.