Diezani: 'Yan majalisa na tsaka mai wuya

Ministar mai ta Nigeria, Diezani Alison Maduke Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sa ran majalisar za ta fitar da matsaya game da umarnin kotun nan gaba

Wani dan majalisar wakilan Nigeria ya ce umarnin kotu na dakatar da binciken ministar mai, Diezani Alison-Madueke ya sanya su cikin tsaka mai wuya.

Onorable Jerry Manwe ya yi nuni da cewa 'yan Najeriya za su ga ba sa yin aikinsu, a waje daya kuma kotu ta dakatar da su.

Inda ya kara da cewa ko da yake kundin tsarin mulki ya ce babu wata kotun da za ta hana su aiki, muddin suna aiki ne a kan ka'ida.

A mako mai zuwa ne ya kamata ministar ta bayyana a gaban wani kwamitin majalisar, domin ba da bahasi kan zargin kashe naira 10 biliyan wajen kula da jirgin sama na haya.

Babbar kotun wadda ke zamanta a Abuja ta dakatar da majalisar daga binciken ne, har sai kammala karar da ministar da kuma NNPC suka shigar a gabanta.