'Yan gudun hijira sun zarta miliyan 50

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane miliyan 33.3 ke gudun hijira a cikin kasashensu

Yawan mutanen da ke gudun hijira a sanadiyyar yake-yake ko kuma saboda ana muzguna musu ya zarta miliyan 50 a shekarar 2013, alkaluma irinsu na farko tun bayan yakin duniya na biyu, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Baki daya adadinsu dai ya kai miliyan 51.2 ne, kuma sun rubanya na shekarar 2012 da miliyan shida, a cewar wani rahoto na hukumar.

Antonio Guterres shi ne shugaban hukumar UNHCR kuma ya gaya wa BBC cewa hakan karin "Wani kalubale ne babba" ga kungiyoyin agaji.

Yake-yaken da ake yi a Syria da Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da kuma Sudan ta Kudu ne suka janyo matukar karuwar 'yan gudun hijirar.

"Tashe-tashen hankula na karuwa, sannan wadanda aka dade ana fama da su ba a kawo karshensu ba" Inji Mr. Gutterres.

Abu mafi damuwa kuma shi ne batun 'yan gudun hijira miliyan 6.3 wadanda suka kwashe shekaru suna cikin wannan yanayi.

Asarar da yaki da kuma azabtarwa ke haifar wa ga al'umma

51.2m

mutanen da aka tilastawa barin gidanjensu a fadin duniya

  • 2.6m mutanen da suka tsere daga Afghanistan

  • 1.6m yan gudun hijiran Pakistan

  • 1.2m mutane masu neman mafakar siyasa a fadin duniya

GETTY

Mutanen da suka dade a sansanonin 'yan gudun hijira sun hada da 'yan Afghanistan miliyan 2.5.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kada a tilastawa 'yan gudun hijira komawa kasashensu, har sai komai ya daidaita kuma sun samu matsugunai.

Don haka ga 'yan Somaliya 300,000 da ke sansanin Dadaab a Kenya, abu ne mai kamar wuya.

Sai dai mutanen da ke gudun hijira a cikin kasashensu sun ninnika wadanda suka bar kasashensu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A kasar Syria kadai akwai 'yan gudub hijira miliyan 6.5 wadanda ke fuskantar matsanancin karancin abinci da ruwan sha da magunguna da matsugunai, saboda ana cigaba da gwabza fada a wuraren da suke.

Mr. Guterres ya kara da cewa "Babu mafita da dan adam zai samar game da matsalolin rayuwa da 'yan gudun hijirar ke fuskanta. Kuma abin takaici shi ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya kasa yin komai wajen kawo karshen yake-yaken da ake fama da su."