Ana zaben gwamna a Jihar Ekiti

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mutane a Jihar Ekiti dake kudu-maso-yammacin Najeriya na kada kuri'a a zaben gwamnan jihar da ake yi ranar Asabar din nan.

Tunda safe ne masu kada kuri'a suka fara yin layuka a runfunan zabe, inda aka rika tantance sunayen su domin basu damar yin zaben.

'Yan takara 18 ne suka shiga zaben, amma fafatawar tafi karfi ne tsakanin gwamnan dake kan gado Kayode Fayemi na jam'iyyar APC da dan takarar jam'iyyar PDP tsohon gwamnan jihar Ayo Fayose da kuma na jam'iyyar Labour Opeyemi Bamidele.

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta ce masu kada kuri'a fiye da dubu 700 ne keda damar yin zaben. Ta kuma ce ta an rarraba kayan zaben ko-ina domin gudanar da shi lami lafiya.

An dauki tsauraran matakan tsaro a dukkan fadin jihar, inda jami'an tsaro keta shawagi.

Manyan jam'iyyun dake takara a zaben dai na ta zargin junansu da neman yin magudi.

Karin bayani