Al'ummar jihar Ekiti na zaben Gwamna

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria INEC ta ce masu kada kuri'a kimanin dubu 700 ne za su gudanar da zaben gwamna a tsakanin 'yan takara 18 a jihar Ekiti ranar asabar din nan.

Hukumar ta ce tuni ta raba kayayyakin zabe a fadin kananan Hukumomin jihar inda za su isa gundumomin da ke fadin jihar a kan lokaci, baya ga ma'aikata sama da dubu 8 da 400 da ta dauka aiki.

Mukaddashin mai magana da yawun Hukumar zabe ta kasa, Nick Dazang ya ce Hukumar ta bullo da sabbin tsare-tsare da za su hana yin magudi a wannan zabe da manyan jam'iyyun PDP da APC da kuma jam'iyyar Labour ke fafatawa.

Ya ce za a bude rumfunan zabe da karfe 8 na safe agogon Nijeriya, inda za a fara tantance masu zabe har zuwa 12 na rana, kuma da zarar an kammala kada kuri'a za a kidaya kuri'u kuma a fitar da sakamako a cibiyar da aka yi zabe.

Ya ce ya yi imani da irin tanadin da Hukumar ta yi za a fitar da cikakken sakamakon zabe