Iran ta soki shigar Amurka rikicin Iraqi

Image caption Ayatullah Khamene'i, jagoran addini na Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce yana matukar adawa da duk wani yunkuri da Amurka da ma kowacce kasa za ta yi na tsoma baki a abin da ke faruwa a Iraqi.

Kamfanin dillacin labaran Iran ya mabato Ayatollah Ali Khamenei na cewa, gwamnatin Iraqi da kuma shugabannin addininta za su iya shawo kan matsalar da take ciki.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban din Iran, Hassan Rouhani, ya yi kakkausar suka ga wasu kasashen larabawa da suke tallafawa masu tada kayar baya 'yan Sunni a Iraqi.

Shugaba Rouhani ya ce, a karshen 'yan ta'adda zasu juya ne su wargaza kasashen dake tallafa musu yanzu haka.

Iran tana zargin Saudiyya da tallafawa mayakan 'yan Sunni.