Mayaka sun dunfari Bagadaza

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mayaka 'yan Sunni sun kame wani muhimmin wurin ketara iyaka tsakanin Iraqi da Syria, sun kuma cigaba da dunfarar birnin Baghadaza.

Wakilin BBC yace wannan nasara da 'yan tawayen suka samu za ta ba su kofar shiga da fitar da makamai ga mayakansu a Iraki da kuma Syria.

Mayakan sun ce sun shigar da motocin soja da dama ta cikin garin Rawa.

Mayakan 'yan Sunni sun kuma kame wasu garuruwan a lardin Anbar.

Masu aiko rahotanni sun ce abinda mayakan suke shirin yi shi ne, shirya kaddamar da farmaki akan birnin Baghadaza.

Karin bayani