Za a kara wa Rasha takunkumi kan Ukraine

Image caption Amurka ta ce abin damuwa ganin yadda Rasha ke kara jibge dakaru a kan iyaka

Amurka ta ce ita da Faransa da Jamus sun amince su wa Rasha sabbin takunkumi, sai fa idan ta dauki matakai cikin gaggawa na rage tunzuri a kan iyaka da Ukraine.

A juma'ar nan ma Amurkan ta kakaba wasu takunkumi kan jagorori 'yan-a-ware 7 masu goyon bayan Rasha a cikin Ukraine ciki har da 'yan tawayen da ke kiran kansu a matsayin magadan wasu garuruwa.

Tun da farko gwamnatin Ukraine ta yi shelar tsagaita wuta nan take tsawon kwanaki 7, lamarin da Hukumomin Moscow suka yi watsi da shi a matsayin wani wa'adi ga 'yan-a-ware.

Amurka ta yi gargadin cewa ba za ta laminci shigar dakarun Rasha cikin Ukraine ba.

Sakataren yada labarai a fadar White House, Josh Earnest ya ce sun damu matuka da alamun jibge dakarun Rasha da suke gani a kan iyakokin Kasashe