Yaki da karancin kudan zuma a Amurka

Image caption Ana fuskantar karancin ruwan zuma a Amurka

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta kafa wata hukuma da zata magance raguwar ruwan zuma.

Hukumar kare muhalli da kuma sashen kula da ayyukan gona ne zasu jagoranci wannan yunkuri.

An kuma ware dala miliyan 8 saboda a samar da sabbin nau'in kudan zuma

A lokacin hunturun da ya wuce an samu raguwar kudan zuma da kashi 23 cikin 100, an kuma alakanta hakan da wasu dalilai da suka hada da magungunan kashe kwari

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce ruwan zuma na karawa abincin da Amurka ke nomawa kima ta fiye da dala biliyan 15

Hakazalika ana kuma danganta raguwar kudan zuma da wasu dalilai da suka hada da rashin wadataccen abinci da kuma cututtuka

Wasu kungiyoyin kare muhalli sun soki Shugaban Kasar Amurka saboda rashin daukar mataki na kai tsaye akan wasu magungunan kashe kwari da ake alakanta su da kashe kudan zuma.