PDP ta lashe zaben gwamna a jihar Ekiti

Image caption Jam'iyyar ta PDP ta samun nasara a dukkanin kananan hukumomin jihar 16.

Hukumar Zabe a Najeriya ta ayyana dan takarar jam'iyya mai mulki ta PDP a zaman wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Ekiti ranar Assabar.

Babban baturen zaben Farfesa Isaac Uzonma ya ce dan takarar jam'iyyar ta PDP kuma tsohon gwamnan jihar Ayodele Peter Fayose ya samu kuri'u 203, 090 daga cikin kuri'u kimanin 369, 257 da aka jefa a zaben.

Wannan na nufin dai Mr.Fayose ya doke babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar mai ci, Kayode Fayemi na jam'iyyar APC wanda ya samu kuri'u 120, 433 a zaben.

Mr. Fayemi ya zamo gwamnan jihar ne a watan Oktoba na shekara ta 2010; bayan da wata kotu daukaka kara ta bayyana shi a zaman wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na shekara ta 2007; abin da ya kawo karshen mulkin wanda ya gada Mr. Olusegun Oni.

Karin bayani