An kera babur mai aiki da lantarki

Hakkin mallakar hoto harley davidson
Image caption Baturinsa yana daukar mintuna 30 zuwa sa'a daya yana caji

Shahararren kamfanin nan mai kera babura Harley-Davidson ya fitar da babur mai amfani da wutar Lantarki a karon farko.

Wannan babur din da aka sakawa sunan Project Livewire zai iya yin tafiyar mil 130 kafin ya bukaci a sake yiwa baturinsa chaji.

Sai dai ba a fara sa shi a kasuwa ba a halin yanzu, maimakon haka kamfanin zai zazzabo wasu abokan huldarsa daga Amurka da za su hau babur din sannan su yi masa bayanin yadda suka ji shi.

Babur din zai hau titin Route 66 na Amurka inda zai ziyarci fiye da abokan huldar kanfanin sama da talatin a tsakanin karshen wannan shekara.

Karin bayani