'Yan siyasar Iraqi basu da tabbacin murkushe ISIS

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Burin mayakan ISIS shine su kame Bagdad

Manyan 'Yan siyasa a babban birnin Iraqi na Bagdad sun yi wani hasashe da ya nuna suna da rashin tabbas, a yadda suke ganin za'a murkushe mayakan Islama na ISIS.

Wakilin BBC dake babban birnin kasar Iraqin Bagdad , yace manyan 'yan siyasar da kuma ma'aikatan diplomaciyar da ya zanta da su, sunyi imanin cewa mayakan ISIS sunfi sojojin Iraqin samun horo, da kuma kayan yaki.

Majiyoyi sun bayyana masa cewa Amurkawa na gudanar da aikin leken asiri ne kawai akan kungiyar ta ISIS tsawon makonni biyu, duk kuwa da irin damuwar da suke da ita game da kungiyar tun watanni 18 dinda suka gabata.

Mayakan sa-kai 'yan sunni karkashin inuwar kungiyar ISIS sun kara samun nasarori a yammacin kasar Iraki, bayan da suka kama babban mashigin kan iyakar kasar da Syria da kuma garuruwa da yawa a kuryacin kasar daura da birnin Bagdaza.