An yanke wa 'yan Al Jazeera shekaru 7 a kurkuku

Ma'aikatan Gidan Talabijin na Al Jazeera Hakkin mallakar hoto Aljazeera
Image caption Mohammed Fahmy da Baher Mohamed da kuma Peter Greste sun musanta zargin da ake musu

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa ma'aikatan gidan talabijin na Al Jazeera uku hukuncin shekaru bakwai a gidan kaso.

Kotun ta yanke hukunci ne bayan ta same su da laifin yada labaran karya da kuma taimaka wa kungiyar 'yan uwa Musulmi.

Daya daga cikin 'yan jaridun da aka yanke wa hukuncin shi ne Peter Greste dan kasar Australiya kuma tsohon ma'aikacin BBC.

Hakan na zuwa ne bayan firai Ministan Australia, Tony Abbot ya roki Shugaban Masar Abdul Fatah Al Sisi, a saki Peter Greste wanda ya ce ba shi da laifi.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba