ISIS ta kwace filin jirgin saman soji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption ISIS dai ta ce babban wurin da ta ke hari shi ne birnin Bagdaza.

An tabbatar da cewa mayakan Sunni wadanda kungiyar ISIS ke jagoranta a Iraqi, sun kwace filin jirgin saman soji da ke garin Tal Afar.

Babban titin daya taso daga iyakar Syria zuwa Mosul, ya bi ta garin na Tal Afar ne mai muhimmanci kuma gari na biyu mafi girma a Iraqi.

Labarin kama filin jirgin Tal Afar na zuwa ne kwana guda, bayan da 'yan bindigar suka kwace ikon iyakokin kasar da Syria da kuma Jordan, bayan sun karbe mashigin kasar dake lardin Anbar na yammacin Iraqin.

Wani wakilin BBC a arewacin Iraqi yace kwace filin jirgin na Tal Afar, wani babban koma baya ne ga gwamnatin Kasar, yayin da suke fatan amfani da shi wajen sake- kwace ikon garin Mosul.

Karin bayani