Mutane takwas sun mutu a harin Kano

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin

Hukumomi a Kano sun tabbarda rasuwar mutane akalla takwas sakamakon tashin bam a makarantar koyon aikin kiwon lafiya, watau School of Hygiene, wadda ke kan titin Jami'ar Bayero.

Bayanai sun nuna cewar wasu mutane da dama sun samu raunuka a daidai lokacin da sabbin dalibai ke rijastar soma karatu a makarantar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Magaji Musa Majiya ya ce an kama wani mutum da ake zargi da hannu a kai harin.

Shaidu a makarantar sun ce sassan jikin mutane watse a kusa da inda bam din ya fashe.

Tuni jami'an tsaro suka killace wurin a yayinda ake daukar wadanda suka ji rauni zuwa asibitoci.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin.

Sai dai kungiyar Boko Haram a baya ta kaddamar da hare-hare a jihar Kano musamman a watan Junairun 2012 inda mutane kusan 200 suka rasu.