Fyade: Zanga-zanga a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu na ganin cewar ba a hukunta masu fyade yadda ya dace.

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi maci a cikin garin Busia da ke yammacin Kenya, suna neman a yi adalci a shari'ar wata yarinya wacce aka yi wa gungun fyade.

A ranar Talata ne ake sa ran za a fara shari'ar wadanda ake zargin sun yi mata fyaden.

Batun ya gamu da sukar kasashen duniya, bayan 'yan sanda sun sa mutane ukun da ake zargi su nome kewayen wani caji ofis a matsayin gwale-gwale.

A bara ne dai wasu maza shida suka auka wa yarinyar mai 15, inda suka yi mata duka sannan suka yi mata fyade.

Mutanen sai suka jefa yarinyar cikin kwata inda ta samu raunuka a bayanta da cikin jikinta.

Karin bayani