Yunwa na halaka yara kanana a Borno

Gwamna Kashin Shettima na Borno
Image caption Kananan yara a Borno na fama da karancin abinci mai gina jiki saboda rashin tsaro.

Rahotanni daga jahar Borno dake arewacin Najeriya na cewa jama'a da dama ne yanzu haka ke cikin kangin yunwa a yankin kudancin jahar

Wannan al'amari na yunwa ya fara hallaka yara kanana.

Rashin samar da wadataccen abinci mai gina jiki a yankin, nada nasaba da tashe- tashen hankulan 'yan kungiyar Boko Haram.

Wani dan Majalisar dattijan Nigeria dake wakiltar yankin ya shaidawa BBC cewa manoma basa iya gonakinsu abinda yasa aka shiga matsalar karancin abinci.

'Abinda yake faruwa a jahar Borno yafi karfin hukumar bada agajin gaggawa, ya kamata ayi shiri na musamman ' in ji Senator Ali Ndume.