Mutane 21 ne suka mutu a harin Abuja

Image caption Hayaki ya turnuke sararin sama a lokacin da aka kai harin

Akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu a harin bam din da aka kai Emab Plaza a Wuse II da ke Abuja babban birnin Nigeria.

Haka kuma wasu mutanen da dama suka samu raunuka, inda rahotanni suka ce mutane 52, yayin da masu aikin gaggawa ke ci gaba da ayyukan ceto.

Harin dai ya auku ne a lokacin da mutane ke hada-hada a rukunin shagunan na Emab.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ji karar fahewar wani abu kuma sun ga mutane na barin wurin da jini a jikinsu.

Karin bayani