BBC ta yi gangami kan daure 'yan Al Jazeera

Image caption Firai Minista Tony Abbot na Australia ya yi kira ga shugaban Masar game da Mr. Greste

Daruruwan ma'aikatan BBC ne suka yi zanga-zangar lumana a gaban ofishinsu da ke London, domin nuna rashin amincewa da hukuncin daure 'yan jarida uku na Al Jazeera.

Ma'aikatan dauke da kwalaye, wasu bakinsu a like sun yi tsit na minti guda, domin adawa da daurin shekaru bakwai da aka yankewa 'yan jaridar a kasar Masar.

Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ya ce ba zai tsoma baki a kan hukuncin da kotun ta yanke ba, duk kuwa da sukar da kasar ke fuskanta daga kasashen waje.

A ranar Litinin ne wata kotu a Masar ta yanke wa Peter Greste da Mohammed Fahmy da kuma Baher Mohammed hukuncin daurin, bayan sun shafe watanni a tsare.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba