MSF ta yi gargadi game da Ebola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana bukatar a gudanar da gangami kan cutar Ebola

Annobar cutar Ebola na ci gaba da samun gindin zama a Kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia.

Kungiyar bayar da gudumawar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce ta duba mutane 470 da suka hada da mutane 215 da aka tabbatar suna dauke da cutar tun watan Maris din da ya gabata.

Kungiyar ta Medecins Sans Frontieres ta yi kira ga gwamnatoci a kasashe ukun da abun ya shafa da su gudanar da babban gangamin fadakarwa a kan cutar.

Haka kuma kungiyar mai zaman kanta ta bayyana cewar a halin yanzu albarkatun ta sun ragu matuka.