Google na gwajin rijistar adireshi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Google ya ce sai wanda ya gayyata ne zai iya amfani da wannan sabon tsarin na gwaji

Kamfanin Google ya bayyana wani shiri na fito da nasa gurbin rijistar adireshin intanet.

Google na gwajin wani gurbi da zai ba abokan huldarsa damar bincikowa da saye da kuma daukar sunayen adireshin shafin intanet da kamfanoninsu za su iya amfani da su.

Ana samun karuwar kamfanonin da ke neman bude nasu shafukan intanet din, abin da ya sa yawan bukatar sunayen ya karu.

Yunkurin na Google dai ya zo ne a daidai lokacin da kamfanin GoDaddy ke neman izinin tara & 100 miliyan ta hanayar sayar da hannayen jari.

GoDaddy na daya daga cikin manyan kamfanonin da ke rijistar adireshin intanet a duniya.

Yunkurin na Google ya sa ya zama abokin gogayyar GoDaddy, wanda a bara ya ke da adireshin intanet miliyan 57 da ya ke kula da su, sannan ya samu kudin shiga &1.1 biliyan.

Google dai na daya daga cikin shafukan matambayi-ba-ya-bata da ake da su a duniya.

Karin bayani