Iraki: 'Yan tawaye sun kama matatar mai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iraki dai ta kasance kasa ta biyu a arzikin mai a duniya.

'Yan tawaye mabiya sunna sun ce sun kama matatar mai mafi girma a Iraki da ke garin Baiji arewa ga birnin Bagdaza.

'Yan tawayen dai sun kwashe kwanakki 10 suna yi wa matatar man kawanya kodayake an yi ta kau da hare-haren suke kai wa.

Matatar ce kan samar da sulusin tataccen man da Iraki ke fitarwa kuma har yakin ya kai ga an fara kayyade wa mutane yawan man fetur din da suke iya saye.

'Yan tawayen karkashin tutar kungiyar ISIS sun kama wurare masu tarin yawa a arewa da kuma yamma ga birnin Bagdaza cikin har da birni na biyu mafi girma a kasar, Mosul.

Karin bayani