Mutane biyar sun mutu a harin Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Al Shabab ta sha kai hare-hare a sassan kasar ta Kenya

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wani harin da aka kai a wani kauye da ke gabar teku a kasar Kenya.

Jami'ai sun ce wasu mutane ne dauke da makamai ne suka afka wa kauyen Witu da ke da nisan kilomita 15 daga Mpeketoni a makon jiya.

Kungiyar masu fafutuka ta Somalia, Al Shabab ta dauki alhakin harin da aka kai a makon jiyan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 60.

Sai dai shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, ya dora laifin harin ne a kan 'yan siyasa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba