Nijar: 'Yan sanda na cafke masu cinikin jarirai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daga cikin mutanen da aka kama, akwai wanda aka samu da jaridai shida.

A jamhuriyar Nijar hukumar 'yan sanda ta PJ na ci gaba da kame mutanen da gwamnatin kasar ke zargin suna da hannu a cikin badakalar cinikin jarirrai

Ana dai zargin ana gudanar da wannan mummunar harka daga Nijeriya zuwa Nijar, dama wasu kasashen yammacin Afrika.

Hukumar 'yan sandan ta kamo wani tsohon karamin jakadan Nijar a Kasar Benin dake ci gaba da rayuwa a Kasar bisa zargin yana da hannu a badakalar cinikin jariran.

Daga cikin mutanen da aka kama, akwai wanda aka samu da jaridai shida.

Hukumomin Nijar dai basu fito sunce komai ba game da wannan lamari.