An kawo karshen yajin aiki a Afruka ta Kudu

ma'aikatan hakar ma'adinai a Afruka ta Kudu Hakkin mallakar hoto
Image caption Ma'aikatan sun ce sassantawar wata nasara ce a garesu

A Afurka ta kudu an kawo karshen yajin aiki mafi tsawo da kuma haddasa asara ga fannin hakar ma'adinan kasar, inda shugabannin ma'aikatan hakar ma'adinan da kuma masu kamfanonin suka sanya hannu akan wata 'yarjejeniya.

Yajin aikin na watanni biyar ya haddasawa kamfanonin hakar ma'adinan asarar kimanin dalar Amurka biliyan biyu, kuma lamarin ya kawo cikas ga tattalin arzikin Afirka ta kudu.

Kungiyoyin ma'aikatan dai sun bayyana sasantawar a matsayin wata nasara da suka samu, amma kuma masu kamfanonin hakar ma'adinan sun ce, lamarin nasara ce ga dukkan bangarorin.