An kakkabo helikwabtan sojin Ukraine

Helikwabtan sojin Ukraine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Helikwabtan sojin Ukraine

Hukumomin Ukraine sun ce, mutane tara aka kashe yayin da aka kakkabo wani jirgin sama na soja a kusa da garin Sloviansk wanda ya ke karkashin ikon 'yan tawaye.

Wannan hari dai ya auku ne kwana guda bayan masu tada kayar baya magoya bayan Rasha sun ce, sun amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da gwamnatin Ukraine ta gabatar. Wakilin BBC ya ce, "Gwamnatin Ukraine da ma kasashen yamma suna zargin Rasha da bada kofa ana shigar da makamai da mayaka cikin Ukraine."

Kafin ma a kai ga wannan dai shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci majalisar dokoki ta soke izinin daukar mataki a Ukraine da aka baiwa dakarun Rashan.

Karin bayani