Google zai fara sayar da agogon komai da ruwanka

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Agogon zai rika alaka da wayar salular mai shi.

Kamfanin Google ya bayyana samfurin agogonsa na komai da ruwanka mai amfani da manhajar Android da zai fara sayarwa.

Daga jerin abubuwan da agogon ke yi har da nuna wa mutum hanya da ba da muhimman bayanai da watsi da kiran waya ta hanyarsa da muhimman abubuwa na bukatar mutum.

Agogon da ya kunshi sanfurin LG G da kuma Samsung Gear Live ana ganin za su samu karbuwa sosai da zarar an fara sayen su.

Samfurin LG wanda za a fara sayar da shi a kasashe 12 da suka hada da Amurka da Birtania da Faransa da Jamus da kuma Japan za a rika sayar da shi kan dala 229.

Mqi agogon zai iya sarrafa shi ta hanyar magana domin bashi umarnin gudanar da wani abu da yake bukata kamar yadda tabaran Google yake.