An zargi Google da hallaka mutane

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mazauna birnin San Francisco na kokawa da tsadar rayuwa da kamfanin suka ce na haifar musu

Masu zanga zanga sun yi Allah-wadai kan yadda kamfanin Google ke kirkiro abubuwan fasaha.

Sau biyu masu zanga zangar ke kawo cikas a lokacin babban taro na shekara-shekara na kaddamar da kayayyakin fasahar da kamfanin ke kirkirowa.

Wata mata na rike da kwali ne da ke dauke da rubutun cewa, ''a inganta hankali'' yayin da wani ke cewa, ''kamfanin na kirkirar na'urorin da ke kashe mutane.''

A shekarar da ta wuce kamfanin na Google ya sayi kamfanin Boston Dynamics, wanda a baya ya kirkiro wa sojojin Amurka mutum mutumi mai siddabaru daban-daban.