Motoci za su fara shawagi ta sama a Tel Aviv

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Motocin za su rika gudun da ya kai kilomita 70 cikin sa'a daya.

Za a dasa wani layin sufurin motoci masu kai-komo a sararin sama cikin birnin Tel Aviv na Isra'ila.

A cewar skyTran, kamfanin da zai gudanar da aikin, za a samar da wani layin sufurin motocin a sama da zai karade harabar Masana'antun Israel Aerospace wanda motocin za su rika zirga-zirga, kafin a bunkasa tsarin don sufurin jama'a.

Kamfanin ya ce wani layin karfe mai maganadisu ne zai rike motoci masu daukar mutane bibbiyu a sama, a matsayin wata sabuwar hanyar sufuri maimakon amfani da titunan kasa masu cunkoso

Ana sa ran kammala dasa layin sufurin kuma a fara amfani da shi a karshen shekara mai zuwa.

Kamfanin na fatan samun nasarar wannan aiki ta yadda zai kai ga samar da samfuri wannan layin mota don daukar fasinjoji

Karin bayani