Wani matashi ya yi ridda a Kano

Image caption Mubarak Bala dai yana da digiri a fannin kimiyyar harhada sinadarai

Iyayen wani matashi a birnin Kano da ke arewacin Najeriya sun kai shi asibitin masu tabin hankali, domin bincike lafiyarsa bayan da kwatsam ya ce shi bai yi imani da Allah ba.

Yanzu haka dai Mubarak Bala mai shekaru 29 na can a tsare a asibitin masu tabin hankali, bayan danginsa wadanda Musulmi ne sun nemi a bincika ko wani abu ne ya taba lafiyarsa.

Sai dai ya samu ya rika yada halin da ya shiga ga duniya ta shafinsa na twitter ta hanyar amfani da wata waya da aka kai masa a sace a asibitin.

Abin da ya ja hankalin wata kungiya mai da'awar kare hakkin wadanda ba su da addini mai suna International Humanist and Ethical Union, wadda ta shiga kiran a sake shi.

Karin bayani