Fira Ministan kasar Poland ya samu galaba

Fira Ministan Poland Donald Tusk Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fira Ministan Poland Donald Tusk

Fira Ministan Poland ya samu galaba a kuri'ar amincewar da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada, bayan kiraye-kirayen ya sauka daga mulki.

Hakan kuwa ya biyo bayan wasu hirarrakin na abin kunya a tsakanin wasu manyan jami'an gwamnati da aka nada a cikin sirri.

Fira Ministan Poland Mr Tusk ne dai ya yi kira ga majalisar dokokin kasar ta da su kada kuri'ar amincewar samun karfin iko, inda ya ce yin hakan na da matukar muhimmanci.

Bayan kada kuri'a ne Kakakin Majalisar Dokokin Ewa Kopacz ta ce, Fira Ministan zai iya maida hankalinsa kan ganawa da shugabannin kasashen Turai.

Ta kuma ce gwamnatin ta samu karfin ikon da za ta gudanar da harkokinta nan gaba a ciki da wajen kasar, kana da wannan karfin ikon ne Fira Minista Tusk zai yi bulaguro zuwa Brussels.