An saki 'yan arewa 144 da aka tsare a Aba

Jami'an tsaro a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro a Najeriya

A Najeriya, an saki wasu daga cikin 'yan arewacin kasar kusan 500 da hukumomin soja suka kama a garin Aba na jihar Abia.

Hukumomin dai na zarginsu da cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne, saboda abin da suka ce yadda motocin da ke dauke da su suka yi jerin gwano.

Matafiyan sun kunshi maza matasa, kananan yara, da matan aure har da wata amarya, an kuma tsare su ne fiye da kwanaki goma a wani barikin sojoji da ke garin Aba.

Sai dai kuma wani shugaban direbobin motocin da aka kama matafiyan a cikinsu, ya ce bai yi mamakin fara sakin mutanen ba saboda basu da laifin komai.