Ba hoton shugaban kasa a ma'aikatu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yadda ake bauta wa hoton shugaban kasa ya yi yawa, musamman a lokacin mulkina.'

Sabon shugaban kasar Costa Rica Luis Guillermo Solis ya mika wani kudurin doka da ke haramta sa hotunansa a ofisoshin ma'aikata.

Luis Guillermo Solis wanda aka rantsar a watan da ya gabata, ya ce ba ya bukatar wannan dabi'a da ta zama ruwan dare ta makala hotunan shugabanni a ofisoshin gwamnati.

Nasarar da Mr Solis ya samu ta sa ya zama dan takara na farko daga jam'iyya ta uku da za ta shugabanci kasar Costa Rica cikin shekaru fiye da 50.

Shugaban kasar ya fada wa manema labarai cewa, sa sunansa a jikin wani tambarin aikin raya kasa da suka hada da gadoji da tituna yana sa wani irin tunani ga mutane.

Ya ce nan gaba za a rubuta shekarar da aka kaddamar da duk wani aiki ne maimakon sunan gwamnati, kamar yadda ya ke faruwa a yanzu.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mr Solis na jam'iyyar Citizen Action Party (PAC) ya ba da mamaki inda ya samu kaso 31 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben watan Fabrairu.

A zaben ra'ayin jama'a da ya biyo, Mr Solis ya samu goyon baya mai yawa, yayin da abokin hamayyarsa ya dakatar da yakin neman zabe tare da ficewa daga takarar.

Bayan haka, Mr Solis ya ci gaba da yakin neman zabe, inda ya yi alkawarin tabbatar da ganin an yi sahihin zabe da kuma dakatar da kashe kudade barkatai.

Hakkin mallakar hoto Reuters