Yaki da cutar Ebola a yammacin Afirka

Yaki da cutar Ebola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaki da cutar Ebola

Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta ce akwai bukatar daukar kwararan matakai na yaki da yaduwar cutar Ebola mai hallakarwa a kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia.

Hukumar ta WHO ta ce an samu karuwar yawan mutanen da cutar ta hallaka da kuma wadanda suka kamu da ita a cikin makonni ukkun da suka wuce.

Hakan na faruwa duk da cewa an tura kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya zuwa yankin.

Wata wakiliyar BBC ta ce watanni 4 bayan barkewar cutar, yawan mutanen da suka kamu da ita ya zarta 600, kuma kashi 60 daga cikin 100 na wadannan marasa lafiyar sun rasu.

Hakan dai ya nuna cewa wannan ita ce annobar Ebola mafi muni da aka samu ya zuwa yanzu.

Hukumar ta WHO ta kira wani taro na musamman na ministocin lafiya daga kasashe 11 na yammacin Afruka, wanda za a yi a farkon watan gobe a Ghana.