Harin bam: Jonathan ya bar taron AU

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya katse halartar taron kungiyar kasashen Afrika da ake yi a Equatorial Guinea saboda harin bam da aka kai Abuja.

Shugaban ya koma gida Najeriya kwana daya bayan harin da aka kai a rukunin shaguna na Emab ya kashe mutane akalla 21.

Mataimakin shugaban Najeriyar Arch. Namadi Sambo ya kai ziyarar gani da ido inda lamarin ya faru, kana ya ziyarci babban asibitin Maitama domin duba wadanda suka jikkata a sanadiyyar harin.

An tsaurara matakan tsaro a cikin birnin na Abuja, yayin da wasu rahotanni ke cewa wasu sojoji sun harbe wani mutum guda sannan an kama wani.

Ana zargin mutanen biyu da hannu a harin.

Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin na Abuja.