Cutar Ebola na bukatar kwararan matakai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar ta barke watanni hudu da suka wuce kuma tana ci gaba da yaduwa

Ana bukatar daukar kwararan matakai domin hana bazuwar cutar Ebola mai saurin kisa a yammacin Africa, a cewar hukumar Lafiya ta duniya.

Kimanin mutane 400 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar cutar a kasar Guinea da kuma bazuwarta zuwa kasashen Saliyo da Liberia da ke makwabtaka.

Barkewar cutar ne abu mafi girma idan aka yi la'akari da yawan wadanda suka kamu da wadanda kuma suka mutu da kuma yaduwarta.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce "Ta damu matuka" game da yiwuwar kara bazuwar cutar.

A halin yanzu akwai mutane kimanin 600 da suka kamu da Ebola kuma kashi 60 cikin dari na mutanen sun mutu.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba