Musulmi sun fara azumi a Najeriya

Image caption Musulmai a Najeriya sun fara azumin watan Ramadan

Jama'r Musulmi da dama sun tashi da azumin Ramadan a Najeriya bayan da aka ba da sanarwar ganin watan.

Sai dai akwai wasu da ba su tashi da azumin ba saboda a cewarsu ba su ji sanarwar da aka yi a daren jiya ba.

Fadar Sarkin Musulmi na Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar na ukku ne ta ba da sanarwar.

An ce anga watan ne a Sakwkwato da Argungu da Jigawa da kuma Gwandu.

Wasu musulmi a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa, sun shaida wa wakilin BBC cewa su ba su tashi da azumin ba ne saboda ba su ji sanarwa ba.

Tun farko dai an ba da sanarwwar cewa ranar Lahadi ne ake saran fara azumin na bana.

Watan Ramadan, wata ne mai girma a addinin Musulunci inda Musulmai ke neman gafara da neman yardar Allah Ubangiji Madaukakin Sarki.

Karin bayani