EU za ta share wa Birtaniya hawaye

Hakkin mallakar hoto
Image caption David Cameron da Jean-Claude Juncker

Shugabannin Tarayyar Turai sun yi alkawarin, magance damuwar Birtania, kan yadda tarayyar za ta kasance a nan gaba, bayan zaben Jean-Claude Juncker, a matsayin shugaban hukumar tarayyar na gaba.

Frai ministan Birtaniya, David Cameron ya ce shawarar nada Mr Juncker, wanda ya kira dan cikin gida a kungiyar, yayin da jama'a ke son ganin sauyi a cikinta, ta sa da wuya Birtania ta ci gaba.

Frai ministan Sweden Fredrik Reinfeldt ya gaya wa BBC cewa, zaman Birtania a kungiyar abu ne mai muhimmanci, kuma zai yi kokarin ganin an aiwatar da sauye-sauyen da London ke son a yi.